Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin ya bayyana cewa, kasar Sin ta yi kira ga Isra’ila da ta gaggauta dakatar da ayyukan soji da take yi, tare da dakile wani mummunan bala’in jin kai a yankin Rafah na Gaza.
Kakakin ya bayyana hakan ne Talatar nan, a lokacin da aka bukaci ya yi karin haske kan ra’ayin kasar Sin dangane da munanan hare-haren da Isra’ila ta kai a birnin Rafah dake kudancin Gaza, wanda ya haddasa hasarar rayuka da dama, da kuma shirin da sojojin Isra’ila suke yi na kai farmaki ta kasa kan Rafah.
Kamfanin dillancin labaran Palasdinu ya bayyana cewa, da sanyin safiyar jiya ne Isra’ila ta kaddamar da hare-hare ta sama da ruwa da kuma ta kasa a Rafah da ke kudancin zirin Gaza da kuma yankunan da ke kewaye, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar mutane sama da 100. A cewar majiyoyin yankin, an shafe kusan mintuna 30 zuwa 40 ana kaddamar da hare-haren, da nufin kubutar da wasu fursunoni biyu da ke hannun kungiyar gwagwarmayar Islama ta Hamas.(Ibrahim)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp