Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin ya shaida a gun taron manema labarai da aka gudanar yau Litinin cewa, Sin tana taya sabuwar gwamnatin Palasdinu karkashin jagorancin Mohammad Mustafa, firaminista kana ministan harkokin wajen Palasdinu, murnar rantsuwar kama aiki. Kuma tana kira ga kasashen duniya da su goyi bayan hukuma ikon al’ummar palasdinawa wajen karfafa iko, da ingiza bangarorin siyasa don su sulhunta ta hanyar shawarari, ta yadda za su amince da sabuwar gwamnatin.
Wang Wenbin ya kuma jadadda cewa, Sin za ta ci gaba da hadin gwiwa da kasashen duniya don gaggauta tsagaita bude wuta da kiyaye fararen hula, da taka rawar gani kan ingiza magance rikicin Palasdinu ta hanyar kafa kasashe biyu. (Amina Xu)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp