Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Mao Ning, ta ce Sin ta yi maraba, da kuma taya Najeriya murnar zama abokiyar hulda ta gamayyar BRICS. Ta fadi hakan ne yayin da take tsokaci a Litinin din nan, yayin taron manema labarai na yau da kullum, bayan da aka ayyana Najeriya a matsayin kasa ta 9, cikin jerin kasashen da suka zamo abokan kawancen gamayyar ta BRICS.
Mao ta ce Najeriya babbar kasa ce mai tasowa, don haka shigarta jerin kasashe abokan huldar hadin gwiwar gamayyar BRICS, zai bunkasa ci gabanta, da ingiza moriyar bai daya ta kasashe mambobin gamayyar, da abokan huldarta, da sauran kasashe masu tasowa, wanda hakan zai bayar da gudummawar bunkasa tsarin ciyar da ayyukan hadin gwiwar BRICS gaba. (Saminu Alhassan)