Hukumar lura da ayyukan ’yan sama jannati ta kasar Sin ko CMSA, ta ce da sanyin safiyar Talatar nan kasar ta yi nasarar harba kumbon dakon kaya na Tianzhou-9 zuwa tashar sararin samaniya ta kasar wato Tiangong.
An harba kumbon ne da karfe shida saura mintuna 26 agogon Beijing, daga tashar harba kumbuna ta Wenchang dake lardin Hainan na kudancin kasar, ta amfani da rokar Long March-7 Y10.
Rahotanni sun ce mintuna kimanin 10 da harba shi, Tianzhou-9 ya rabu da jikin rokar Long March-7 Y10, inda ya shiga da’irarsa kamar yadda aka tsara. Kazalika, farantan makamashin hasken rana dake jikinsa sun bude, kamar dai yadda hukumar ta CMSA ta bayyana.
Kumbon na Tianzhou-9, ya yi nasarar haduwa da muhimmin sashen Tianhe, babban bangaren tashar binciken sararin samaniya ta kasar Sin watau Tiangong.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp