Kasar Sin ta yi nasarar harba wani sabon tauraron dan Adam na gwaji zuwa sararin samaniya, daga cibiyar harba tauraron dan Adam ta Jiuquan dake yankin arewa maso yammacin kasar.
An harba tauraron ne da misalin karfe 7 na daren jiya, agogon birnin Beijing, ta hanyar amfani da roka Long March-2C, ya kuma shiga cikin falaki kamar yadda da aka tsara.
Za a yi amfani da tauraron ne wajen gudanar da aikin gwajin fasahar intanet na tauraron dan adam.
Wannan shi ne karo na 478 da aka yi amfani da rokar Long March, wajen harba tauraron dan Adam zuwa sararin samaniya. (Mai fassara: Ibrahim)