Da yammacin yau ne kasar Sin ta yi nasarar harba dakin gwaje-gwaje na biyu na tashar binciken sararin samaniyarta da ake kira Mengtian zuwa sararin samaniya, matakin dake kara kusanto ga aikin kammala tashar ya zuwa karshen wannan shekara.
Da misalin karfe 3 da mintuna 37 agogon Beijing ne, aka harba samfurin dakin gwajin na Mengtian ta hanyar amfani da rokar Long March-5B daga cibiyar harba taurarin dan-Adam dake Wenchang na lardin Hainan dake kudancin kasar Sin. (Mai fassarawa: Ibrahim daga CMG Hausa)