Ana sa ran shirya bikin baje kolin kayayyakin da ake shigowa da su kasar Sin karo na biyar wato CIIE a birnin Shanghai, daga ranar 5 zuwa ranar 10 ga wata mai zuwa.
A matsayinta na wadda ta riga ta shiga bikin har na tsawon shekaru biyar, kungiyar kasuwanci ta Hafen Hamburg Marketing e.V ta kasar Jamus, tana fatan inganta hadin kai da bangarori daban daban, don more damar bunkasuwa ta hanyar shiga bikin CIIE, ta yadda za a samu ci gaba tare.
Axel Mattern, shugaban kungiyar kasuwanci ta Hafen Hamburg Marketing e.V yana ganin cewa, bayan ci gaban da bikin CIIE ya samu a cikin shekaru biyar da suka gabata, ya riga ya zama wani muhimmin dandali na nuna yadda kasar Sin ke bude kofa ga ketare don more damar bunkasuwa.
Yana mai cewa, “Bikin CIIE kyakkyawan dandali ne ga masu hada hadar cinikayyar shige da fice, da na zirga-zirga da sufuri, da kuma na rarraba kayayyaki. Don haka muka shiga bikin tun a karo na farko.
A cikin shekaru biyar da suka gabata, wurin da aka ba mu domin nuna kayayyakinmu yana ta karuwa, kuma yawan kamfanonin birnin Hamburg da suke shiga bikin yana ta karuwa, kuma ana ta sabunta na’urorin zamani a gun bikin.”(Kande Gao)