Kamar yadda muka sani, sufuri muhimmin jigo ne a hada hadar rarraba hajoji cikin kasashe, da ma tsallaken kan iyakar sassa daban daban na duniya. Kaza lika hanya ce ta tabbatar da daidaiton farashin kasuwani, wanda kuma ke baiwa ’yan kasuwa zarafin sada kasuwanni da kayayyaki gwargwadon bukatar da ake da ita.
To sai dai kuma, a shekarun baya bayan nan hankula na kara karkata ga raya fannin sufuri, ta amfani da ababen hawa dake amfani da nau’o’in makamashi marasa gurbata yanayi, da kyautata muhallin halittu, da kare lafiyar jama’a musamman a cibiyoyin birane.
- Xi Ya Jaddada Zurfafa Gyare-gyare Don Inganta Kwarewa A Sabbin Fannoni
- Binciken CGTN: Sama Da Kashi 80% Na Masu Amsa Tambayoyi A Duniya Sun Yaba Da Manufar Harkokin Waje Na Sin
Karkashin wannan buri ne kasar Sin ta tashi tsaye wajen aiwatar da sauye sauye, da matakai daban daban na raya fannin sabbin makamashi, ta yadda ya zuwa yanzu kasar ta wuce gaba, a bangaren samar da ababen hawa masu aiki da sabbin makamashi.
A daya bangaren kuma, kasar Sin ta yi namijin kokari wajen taimakawa kasashe masu tasowa, wadanda da yawansu ke a nahiyar Afirka, da fasahohin cin gajiya daga irin wadannan sabbin ababen hawa na zamani. Hakan ya yi matukar taimakawa kasashe da dama a nahiyar wajen rungumar irin wadannan ababen hawa musamman masu amfani da lantarki, ta yadda matakin ke rage adadin iskar carbon mai dumama yanayi da ake fitarwa a kasashen.
Misali a kasar Kenya dake gabashin Afirka, kusan dukkanin ababen hawa dake amfani da makamashin lantarki, ana yin odar su ne daga kasar Sin, matakin da masana ke cewa har ya fara yin tasiri wajen kyautata iska, da rage fitar da hayaki daga motoci da babura dake bin titunan kasar.
Ganin irin alfanun dake tattare da wannan mataki, ita ma gwamnatin Kenya ta samar da manufofi, da tsare-tsaren doka na ingiza cin gajiya daga ababen hawa masu amfani da lantarki, baya ga zuba jari a fannin samar da kamfanonin harhada ababen hawan masu amfani da sabbin makamashi a kasar, irin su motocin bas-bas, da baburan hawa masu kafa 2 da masu 3.
Alkaluma daga kungiyar kamfanonin kirar ababen hawa ta kasar Sin, sun nuna yadda Sin ke fadada fitar da ababen hawa masu amfani da lantarki da makamantansu, inda adadin da kasar ta fitar a bara, ya karu da kaso 77.6 bisa dari, wato karuwar da ta kai ta sama da ababen hawan miliyan 1.2, in an kwatanta da na shekarar da ta gabaci hakan.
Bugu da kari, sashen masana’antar sarrafa ababen hawa masu amfani da sabbin makamashi ta Sin, ya shiga layin fannonin dake taka rawar gani wajen ingiza tattalin arzikin kasar, a gabar da Sin din ta zamo babbar kasuwar ababen hawa masu amfani da sabbin makamashi mafi girma a duniya cikin shekaru 9 a jere, inda take baiwa kasuwar duniya ta wannnan nau’i na ababen hawa gudummawar kaso sama da 60 bisa dari.