Mataimakin babban hafsan-hafsoshin soja, na hedkwatar manyan hafsoshin sojin kwamitin sojan tsakiyar JKS, Laftana Janar Jing Jianfeng, ya ce Amurka na kokarin haifar da fito-na-fito tsakanin sassa daban daban, domin cimma muradun ta na kashin kai, kuma hakan ne ma ya sanya ta sukar kasar Sin a taron tattaunawa na Shangri-La.
Yayin da yake zantawa da manema labarai a Asabar din nan, Laftana Janar Jing Jianfeng, ya ce kalaman sakataren tsaron Amurka Lloyd Austin a yayin wancan taro, da ma wadanda ya yi a baya, na kunshe da yunkurin Amurka na wanzar da salon ta na danniya, da yunkurin kafa tsarin fito-na-fito, ta hanyar kira a kafa kawancen yankin tekun Indiya da Fasifik. (Saminu Alhassan)