A cikin wannan satin ne kungiyar kwallon kafa ta Chelsea ta nada Mauricio Pochet-tino a matsayin sabon kociyanta, wanda zai fara aiki ranar 1 ga watan Yulin wannan shekarar ta 2023.
Kungiyar ta dauki tsohon kocin Tottenham, bayan da ta kammala kakar Premier League ta bana a mataki na 12 kuma mataki mafi muni da kungiyar ta taba tsintar kan-ta sama da shekara 37.
Wanene Pochettino?
Espanyol
Lokacin da yake koyar da kungiyar kwallon kafa ta Espanyol ya jagoranci kungiyar ta kasar Sipaniya adadin wasanni 161 inda ya ci wasanni 53 da canjaras 38 aka doke shi 70. Bayan da Pochetino ya yi ritaya daga buga wa Espanyol wasa a shekarar 2006, dan kasar Argentina ya karbi aikin jan ragamar kungiyar a watan Janairun shekara ta 2009 a lokacin da kungiyar ke fuskantar barin La Liga.
Daga nan ya ceto kungiyar wadda ta kare a tsakiyar teburi – wanda ya ci Barcelona a gasar La Liga da yin canjaras da kungiyar ta a gasar Copa del Rey sannan a kakar wasa ukun da ya ja ragamar Espanyol ta yi ta 11 da ta takwas da kuma ta 14, amma ya bar kungiyar tana cikin ‘yan karshen teburi cikin watan Nuwamba lokacin tana fuskan-tar barazanar tattalin arziki.
Southampton
Bayan da ya koma kasar Ingila da koyarwa, Pochettino ya ci wasanni 23 da canjaras 18 aka doke shi fafatawa 79 bayan da ya karbi aikin horar da Southampton a tsakiyar kaka, bayan da ya maye gurbin Nigel Adkins.
Kocin ya ja ragamar kungiyar ta kammala Premier a mataki na 14 a teburi, sannan a kaka ta gaba Southampton ta yi ta takwas sai dai Pochettino ya yi aikin a lokacin da baya jin turaci, inda ya dauki mai yi masa fassara a lokacin ganawa da ‘yan jarida, am-ma hakan bai hana shi samun nasara ba a Ingila.
Tottenham
Mai koyarwa Pochetino ya samu nasarar lashe wasanni 159 da canjaras 62 aka doke shi 72 sannan a shekara biyar da Pochettino ya yi a Tottenham, kungiyar ta samu na-sara mai yawa a tarihin kafuwarta.
Tottenham ta fara kare kakar Premier League a mataki na biyar da na uku da na biyu da sake yin na uku, sannan ta kammala a ta biyar a teburin babbar gasar firimiya ta Ingila.
Haka kuma a karkashin Pochetino,Tottenham ta kai karawar karshe a Champions League da kuma League Cup sai dai ya hada matasan ‘yan wasa a Tottenham a loka-cin da kungiyar ta yi ta biyu a Premier a kakar 2016 zuwa 2017.
Saboda ya hada ‘yan wasa daga Ingila da suka hada da Harry Kane da Dele Alli da kuma Eric Dier, sannan ya hada da wasu daga waje da suka hada da Christian Eriksen da Son Heung-min da kuma Toby Alderweireld. Tottenham ta dauki masu ko-yarwa 10 a cikin shekara 12 kafin ta dauki Pochettino a 2014 sai dai tun bayan da ta sallami kocin a Nuwambar 2019 daga nan ne abubuwa suka sake komawa baya, inda ta dauki Jose Mourinho da Ryan Mason na rikon kwarya har karo biyu da Nuno Espiri-to Santo da Antonio Conte da na rikon kwarya Cristian Stellini.
Duk da haka Tottenham, wadda ta buga Champions League a bana ta kasa samun gurbin shiga gasar zakarun Turai ta badi, bayan da ita ce ta takwas da maki 60 a kakar bana.
Paris St Germain(PSG)
A zaman da yayi a kungiyar kwallon kafa ta Paris Saint German ya ci wasanni 55 da canjaras 15 aka doke shi wasa 14 sannan ya buga wa Paris St-Germain wasa tsakanin 2001 zuwa 2003, wadda ta dauke shi aikin koci a 2021.
Ya dauki babban kofi a matakinsa na mai horarwa, bayan da ya lashe Coupe de France a kakar 2020 zuwa 2021 da kuma Ligue 1 a shekarar 2021 zuwa 2022 sai dai a kakar 2020 zuwa 2021 PSG ta kare a mataki na biyu, bayan da Lille ta dauki Ligue 1, sannan PSG ta kasa kai wa wasan karshe a Champions League.
Karo na biyu kenan da ta kasa cin babban kofin Faransa a kaka tara, hakan ya sa aka kori Pochettino bayan ya maye gurbin Thomas Tuchel a PSG, lokacin da dan kasar Jamus din ya koma Chelsea, inda ya maye gurbin Frank Lampard.