Alkaluman baya bayan nan da ofishin lura da kare ikon mallakar fasaha na Sin ya fitar, sun nuna yadda Sin ta kasance kan gaba, da bukatar rajistar mallakar fasahar kamfanonin sarrafa farantan samar da lantarki ta hasken rana, wadanda yawan su ya kai 126,400. Da wannan adadi, Sin ta zamo ta daya a duniya, ta fuskar karfin kirkire-kirkire a fannin.
A shekarun baya bayan nan, matsakaicin ci gaban neman rajistar masana’antun kera farantan samar da lantarki ta hasken rana a Sin ya kai kaso 23.1 bisa dari, kana ingancin fasahohin na karuwa, yayin da karfin sarrafa hasken rana zuwa lantarki na farantan da ake sarrafawa a Sin, ya zarce na sauran kamfanoni dake sauran sassan duniya.
- Sin Ta Fitar Da Shirin Bunkasa Cin Gajiya Daga Bayanai Ko Data
- Xi Ya Aike Da Sakon Ta’aziyya Ga Takwaransa Na Iran Bisa Munanan Hare-haren Ta’addanci Da Aka Kai A Kasar
A halin yanzu, wasu sabbin nau’o’in ababen hawa da ake kerawa a Sin, na samar da makamashi da sassan cikin ababen hawan ke bukata, ta fasahar farantan dake kan rufin ababen hawan. Har ila yau, akwai farantar sarrafa hasken rana da ake samarwa, masu taimakawa fasahar hana zaizayewar kasa, da na kiwon tumaki, da na kiwon kifi, da sauran fasahohi masu nasaba.
Wadannan sassa sun fadada kasuwan samar da farantar lantarki ta hasken rana, tare da gabatarwa duniya karin fasahohin Sin na raya ci gaba a wannan fanni. (Saminu Alhassan)