Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin, Guo Jiakun ya bayyana a yau Alhamis 6 ga watan nan cewa, Gaza ta Falasdinawa ce kuma tana daga wani bangare na halastattun yankunan Falasdinawa, don haka ba wuri ba ne da za a yi tayin siyasa da shi ba, ballan tana kuma a ce ta zama fagen wasan kura.
Ya bayyana haka ne a martanin da ma’aikatar ta mayar a kan kalaman da Shugaba Donald Trump na Amurka ya yi a kwanan nan cewa, yana so ya tare da karbe iko da ita.
Guo Jiakun ya bayyana cewa, kasar Sin tana goyon bayan halastaccen ikon al’ummar Falasdinu, sannan a ko da yaushe tana amanna da cewa, “Falasdinawa su mulki Falasdinu” wata muhimmiyar ka’ida ce da ta zama wajibi a yi aiki da ita wajen tafiyar da mulkin zirin Gaza bayan yaki, kuma tana adawa da yunkurin tilasta wa al’ummar Gaza yin gudun hijira da karfin tuwo. (Abdulrazaq Yahuza Jere)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp