Takardar bayanin ta yi nuni da cewa, shawarar “ziri daya da hanya daya” wani kyakkyawan misali ne na gina al’ummar duniya mai makomar bai daya, kuma wani dandali ne na amfanar jama’ar duniya da yin hadin gwiwa da kasar Sin ta samar wa duniya.
A cewar takardar, ya zuwa watan Yuli na shekarar 2023, fiye da kashi 3 bisa 4 na kasashen duniya da kungiyoyin kasa da kasa sama da 30, sun sanya hannu kan yarjejeniyoyin hadin gwiwar shawarar “ziri daya da hanya daya” da kasar Sin.
Takardar ta kara da cewa, shawarar raya kasa ta duniya, da shawarar samar da tsaro ta duniya, da shawarar wayewar kai da kasar Sin ta gabatar, duk sun zama wani muhimmin ginshiki na gina al’ummar duniya mai makomar bai daya.
Kasar Sin ta gabatar da shawarar gina al’ummar duniya mai makomar bai daya, tare da yin kira ga dukkan kasashen duniya, da su samar da kyakkyawar fahimtar juna, da daukar matakan da suka dace, don tinkarar batutuwan da suka shafi duniya, ta yadda za a karfafa gwiwa da himma ga yunkurin dan Adam na samun kyakkyawar makoma.
- Xi Ya Yi Kira Ga Lardin Zhejiang Da Ya Rubuta Sabon Babi Na Inganta Zamanantarwa Ta Sin
- Kasar Sin Za Ta Ci Gaba Da Taimakawa Al’ummar Libya Wajen Yakar Bala’in Ambaliyar Ruwa
Takardar bayanin ta kara da cewa, bisa zurfin tunani, kasar Sin ta fahimci cewa, mabambantan al’adu suna da mabambantan fahimtar yanayin wadannan dabi’u, tana kuma mutunta kokarin da jama’ar kasashe daban-daban suke yi na nazarin hanyoyin ci gaban da ya dace da yanayin kasashensu.
Game da wannan takardar bayani, mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin ya jaddada a wajen taron manema labarai da aka yi a yau cewa, yana fatan takardar bayanin za ta taimaka wa mutane daga bangarori daban-daban da kasa da kasa wajen kara fahimtar ma’anar al’umma mai kyakkyawar makoma ta bai daya, da kara sanin babban burin harkokin diflomasiyya masu salon musamman na kasar ta Sin.
Jami’in ya ce, kasar Sin ce ta bada shawara gami da daukar matakai na zahiri, a fannin raya shawarar “ziri daya da hanya daya”, da bullowa gami da aiwatar da shawarwarin da suka shafi ci gaba da tsaro da wayewar kai na duniya, da kara hada kai tare da kasashe da yankuna daban-daban don gina al’umma mai kyakkyawar makoma ta bai daya.
Jami’in ya kara da cewa, kawo yanzu, akwai wakilai daga kasashe sama da 130 da suka tabbatar da cewa za su halarci babban dandalin tattaunawa na hadin-gwiwar kasa da kasa kan shawarar “ziri daya da hanya daya” karo na uku, yayin da wakilai na kungiyoyin kasa da kasa da dama su ma suka tabbatar da halartarsu. (Masu Fassarawa: Ibrahim Yaya, Murtala Zhang)