Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Lin Jian ya bayyana a ran 19 ga watan da muke ciki cewa, Sin tana dukufa wajen gaggauta tabbatar da duniya mai da hankali kan batun samun bunkasuwa, tana kuma fatan hadin gwiwa da mabambantan bangarori don raya wata duniya mai adalci da ake samun bunkasuwa tare, inda za a kawar da talauci da cimma kyakkyawar fata.
Lin Jian ya ce, shawarar raya duniya baki daya da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar, ta samar da akidar da duniya za ta bi wajen ingiza sha’anin raya duniya da hadin gwiwar kasa da kasa. Sin tana daukar samun bunkasuwa da muhimmanci a G20, da kuma mai da tabbatar da ajandar samun bunkasuwa nan da shekarar 2030 a gaban komai, kana da kulla huldar abota mai dorewa a duniya, da gaggauta samun bunkasuwar duniya da ake yin hakuri da juna da amfanawa daukacin bil Adam mai dorewa. A gun taron kolin G20, Xi Jinping ya gabatar da jawabi kan batun tinkarar yunwa da talauci a mataki na farko, inda ya bayyana dabarar Sin na kawar kangin talauci da yin kira da a kafa wata duniya mai adalci da ake samun bunkasuwa tare. (Amina Xu)