Ofishin kula da harkokin yankin Taiwan na kasar Sin ya kira wani taron manema labarai na yau da kullum a yau Laraba, inda kakakin ofishin Peng Qing’en, ya ce kasar Sin za ta hada kan Sinawan yankin Taiwan da na babban yankin kasar su zama tsintsiya madaurinki daya, kuma tana kan bakanta na yaki da ’yan aware dake nufin ware Taiwan daga kasar Sin, haka kuma za ta kiyaye zaman lafiya a mashigin tekun Taiwan.
Peng Qing’en, ya bayyana haka ne lokacin da yake jaddada kalaman da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yi yayin tattaunawa ta wayar tarho tsakaninsa da shugaban Amurka kan yankin Taiwan, inda ya jaddada cewa dole ne kasashen biyu su hada kai don kiyaye kyakkyawan sakamakon yakin duniya na biyu.
Bugu da kari, game da sanarwar da Japan ta fitar, ta girke makamai masu linzami a wani tsibirin dake da tazarar kilomita 110 kacal daga Taiwan, Peng Qing’en ya bayyana cewa, bangaren Japan na jibge makamai a tsibirin dake kusa da Taiwan da gangan domin haifar da tashin hankali a yankin, da kuma haifar gaba tsakanin sojoji, yana mai bayyana hakan a matsayin mai matukar hadari.
Peng Qing’en ya jaddada cewa, ko shakka babu, Taiwan wani yanki ne na kasar Sin. Kuma kasar ba za ta kyale wasu kasashe su yi katsalandan cikin yankin Taiwan ba, kuma ba za ta yarda Japan ta sake dawo da ra’ayin amfani da karfin soja ba. (Amina Xu)














