Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Mao Ning, ta ce Sin ba ta goyon bayan wani bangare a rikicin Ukraine. Mao, wadda ta bayyana hakan yau Juma’a yayin taron manema labarai da aka saba gudanarwa, ta ce har kullum matsayar Sin ita ce karfafa gwiwar komawa ga tattaunawar wanzar da zaman lafiya.
Jami’ar ta kara da cewa, Sin ta yi rawar gani wajen ingiza bukatar tsagaita bude wuta, da kawo karshen yaki. Kazalika, a cewarta dukkanin sassan kasa da kasa sun kwana da sanin matsayar adalci, da hangen nesa ta kasar Sin, cewa tsawaitar rikicin Ukraine ba zai haifar da ‘da mai ido ga kowa ba.
Har ila yau, a cewar jami’ar, Sin na goyon bayan gaggauta warware batun Ukraine ta hanyoyin diflomasiyya, kuma a shirye take ta ci gaba da taka muhimmiyar rawa tare da sauran sassan kasa da kasa, bisa la’akari da damuwar sassan dake cikin rikicin. (Saminu Alhassan)












