A baya bayan nan, hukumar sadarwa ta Amurka, ta fitar da sanarwa dake cewa, an haramtawa kamfanonin kasar Sin da dama sayar da kayayyakin da ake amfani da su a harkokin sadarwa da na sanya ido a Amurka.
Da yake tsokaci game da hakan, kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Zhao Lijian, ya bayyana a yayin taron manema labarai na yau Litinin cewa, matakin Amurka ci gaba ne da fakewa da batun tsaron kasa wajen keta hakkokin kamfanonin Sin, tare da amfani da karfin iko ba bisa ka’ida ba.
Zhao ya ce Sin na matukar adawa da wadannan matakai, wadanda suka keta ka’idojin cudanyar tattalin arziki, da karya dokokin cinikayyar kasa da kasa, da gurgunta moriyar kamfanonin kasar Sin. (Saminu Alhassan)