Wakilin dindindin na kasar Sin a MDD Fu Cong, ya yi kira da a dakile mummunan yanayin wanzuwar tashe-tashen hankula da yunwa. Fu Cong ya yi kiran ne a jiya Litinin, yayin muhawarar kwamitin sulhu dangane da tashe-tashen hankula da batun karancin abinci.
Fu ya kara da cewa, rikice-rikice na masu dauke da makamai wani muhimmin dalili ne dake haifar da matsalolin jin kai da yunwa. Don haka kasar Sin ke kira ga sassa masu yaki da juna da su shawo kan rikici ta hanyar tattaunawa da shawarwari, a kokarin kawo karshen tashe-tashen hankula cikin hanzari, da maido da zaman lafiya da tsaro.
Jami’in na Sin ya kuma yi kira da a kara azamar samun ci gaba mai dorewa, da magance ainihin dalilin dake haddasa rikici da karancin abinci. Ya ce kamata ya yi kasashen duniya su kara mara wa kasashe masu tasowa baya, wajen kyautata kwarewarsu ta raya kai da shugabancin kasa, a kokarin samun kwanciyar hankali a kasashen.
Fu Cong ya ce, a tsawon lokaci, wasu kasashe masu sukuni kalilan ba sa cika alkawarinsu na bayar da kudaden samar da ci gaba, har ma su kan dakatar da bai wa hukumomin kasa da kasa masu kula da harkokin ci gaba kudade, da fitowa a fili su nuna kin amincewa da ajandar samun ci gaba mai dorewa ta nan zuwa shekarar 2030, lamarin da ya kawo cikas sosai ga sha’anin duniya na samun ci gaba.
Hakan ya sa kasar Sin ta yi kira ga bangarori daban daban, da su tsaya tsayin daka kan manufar cudanyar sassa daban daban, da samar da yanayi mai bude kofa da kwanciyar hankali a duniya wajen samun ci gaba, da gaggauta kawar da gibin ci gaba dake tsakanin kasashe masu tasowa da masu sukuni, a kokarin samun ci gaba tare. (Tasallah Yuan)














