Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin ya yi tsokaci kan yadda gwamnatin kasar Amurka ta sanar da mikawa yankin Taiwan na kasar Sin karin tallafin soja, gami da sayar masa da karin makamai, a yau Lahadi, inda kakakin ya ce, sabon matakin da kasar Amurka ta dauka ya sabawa manufar kasancewar kasar Sin daya tak a duniya, da yarjeniyoyin da Sin da Amurka suka kulla a baya, kan batun Taiwan, lamarin da ya kasance keta hakkin mulkin kai da tsaron kasar Sin. Saboda haka, kasar Sin tana bayyana rashin gamsuwarta ga bangaren Amurka.
A cewar kakakin, batun Taiwan na da matukar muhimmanci, wanda ya shafi moriyar tushe ta Sin. Ya ce tabbas, yadda kasar Amurka ke samar da makamai ga masu neman balle yankin Taiwan daga kasar Sin, zai janyo wa Amurkar asara, kana sam yunkurinta na dakile Sin ta hanyar amfani da batun Taiwan ba zai taba cin nasara ba.
Ban da haka, a jiya Asabar, ofishin kula da yankin Hong Kong na ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin ya yi suka da babbar murya tare da nuna rashin jin dadinsa dangane da wani sabon rahoton da wata hukumar kasar Amurka ta gabatar, wanda ya shafawa yanayin hakkin dan Adam a yankin Hong Kong na kasar Sin kashin kaza. (Bello Wang)