Ma’aikatar harkokin wajen Sin ta bayyana a yau cewa, hukumomin hada-hadar kudi na bangaren Sin na inganta tattaunawa tare da bangaren Kenya, inda bangarorin biyu za su ci gaba da habakawa da zurfafa hadin gwiwa mai amfani a fannoni daban daban kamar zubawa da tattara jari.
Kakakin ma’aikatar Wang Wenbin ne ya sanar da haka yayin taron manema labarai na yau da kullum, lokacin da yake amsa tambayoyi game da hadin gwiwar Sin da Kenya.
- Gwamnatocin Kasashe Da Dama Sun Sake Jaddada Bin Manufar “Kasar Sin Kasa Ce Daya Tak A Duniya”
- Yanzu-Yanzu: Sarki Sunusi Ya Isa Gidan Gwamnatin Kano
Wang Wenbin ya kara da cewa, Sin ta lura da yadda wasu hukumomin hada-hadar kudi na kasa da kasa ke furta kalmomi masu kyau game da tattalin arzikinta, yana mai bayyana karuwar tattalin arzikin Sin a matsayin babban karfi na karuwar tattalin arzikin kasa da kasa.
Game da yanayin bunkasuwar sabuwar tashar kan tudu zuwa teku ta yammacin Sin kuwa, Wang Wenbin ya ce, a halin yanzu, kayayyakin da ake jigilar su ta hanyar, suna zuwa tashoshi 514 na kasashe da yankunan duniya 123.
Bugu da kari, Wang Wenbin ya ce ba za a sauya matsayin al’ummar kasa da kasa kan tsayawa tsayin daka kan manufar kasar Sin daya tak ba, yana mai bayyana manufar a matsayin babban tushen hadin gwiwa tsakanin Sin da sauran kasashe. Ya ce kasar Sin ba za ta yarda da ko wane nau’i na ba da kariya ga ayyukan ballewar Taiwan bisa ko wane dalili ba.
Kana a yau din, kakakin ma’aikatar tsaron kasar Sin, Wu Qian, ya ba da amsa ga ‘yan jarida game da atisayen soja da rundunar sojin ‘yantar da jama’ar kasar Sin reshen gabashin kasar ta gudanar a yankunan teku dake kewayen tsibirin Taiwan. Inda ya bayyana aikin a matsayin mai cikakkiyar ma’ana, dake da nufin yaki da ballewar yankin Taiwan. (Safiyah Ma)