Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Mao Ning, ta ce Sin ta kasance a ko da yaushe mai inganta neman ci gaba ba tare da gurbata muhalli ba, tana cewa cikin shekaru 10 da suka gabata, yawan makamashi maras gurbata muhalli da Sin ta yi amfani da shi ya karu zuwa kaso 17.9 bisa dari na jimillar makamashin da aka yi amfani da shi.
Mao Ning ta bayyana haka ne yayin taron manema labarai na yau Litinin, bayan an yi mata tambaya game da matakan Sin na neman ci gaba ba tare da gurbata muhalli ba.
- Sin Ta Kafa Kungiyar Masana Masu Binciken Sararin Samaniya Mai Zurfi Ta Farko
- China Ta Mayar Da Martani Kan Barazanar Trump Na Ƙarin Haraji Ga Kasashen BRICS
Kakakin ta kara da cewa, cikin shekarun 10 kuma, karfin fitar da hayaki mai dumama yanayi ya ragu da fiye da kashi 34 bisa dari. Tana cewa Sin za ta ci gaba da karfafa hadin gwiwa da kasa da kasa kan tinkarar sauyin yanayi, ta yadda za ta ba da gudummawa ga samun ci gaba mara gurbata muhalli da ma ci gaba mai dorewa.
Da aka tabo batun ziyarar da ministan harkokin wajen Sin Wang Yi ya yi a kasashen Jamus da Faransa a kwanakin baya, Mao Ning ta bayyana cewa, bangaren Sin ya yi farin cikin ganin kasashen Faransa da Jamus, wadanda suke manya a cikin kungiyar EU, sun ingiza EU wajen samun tsare-tsare masu zaman kansu, da samar da fahimta mai adalci da daidaito game da kasar Sin, da warware rikicin tattalin arziki da cinikayya tsakanin Sin da kasashen EU yadda ya kamata, ta yadda suka inganta raya dangantakar Sin da kasashen EU. Ta ce kasar Sin ita ce mai gudanar da ayyuka da kuma ba da gagarumar gudummawa kan inganta ci gaba mara gurbata muhalli, wanda shi ma tushe ne na hadin gwiwarta da kasashen EU.
Bugu da kari, game da barazanar shugaban Amurka Trump cewa za a kara sabon harajin kashi 10 bisa dari ga kasashen kungiyar BRICS, Mao Ning ta ce, tsarin na BRICS ba ya yaki da rukunoni, kuma ba a kafa kungiyar don wata kasa ba. Kana babu mai cin nasara a yakin cinikayya da na haraji, kuma ra’ayin ba da kariya ga cinikayya ba zai samar da mafita ba.(Safiyah Ma)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp