Yau ne mai magana da yawun ma’akatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin ya shirya taron manema labarai na yau da kullum. Wani dan jarida ya yi tambaya game da halin da ake ciki a kasashen Rasha da Ukraine, inda Mr Wang ya ce matsayin kasar Sin kan batun Ukraine bai sauya ba, kuma kasar Sin za ta ci gaba da taka rawa mai yakini wajen warware rikicin cikin lumana ta hanyarta. Kasashen Sin da Ukraine sun ci gaba da tattaunawa yadda ya kamata.
Da yake karin haske kan kalaman da jami’an Amurka suka yi game da batun tambayar da aka yi kan dangantakar dake tsakanin Sin da Rasha, Wang Wenbin ya ce, abin da ya fi daukar hankali shi ne barna da rawar da Amurka ke takawa ke haifarwa wajen tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a duniya. Idan manufar Amurka ta nuna son kai da son zuciya ta ci gaba ko da na kwana daya ne, duniya ba za ta samu zaman lafiya ba. Ya kuma bayyana cewa, Amurka ta sha yada labarin cewa “China na iya baiwa Rasha makamai”. kuma abin da ake kira wai leken asirin ba komai ba ne illa batanci ga China.
Wang Wenbin ya ce, a ko da yaushe Amurka na sako-sako da yadda ake sarrafa kananan makamai da harsasai, kuma ba a martaba ka’ida wajen fitar da kananan makamai zuwa kasashen waje. Amurka ta yi jigilar kayayyakin aikin soji zuwa kasashen waje, da tsoma baki a harkokin cikin gidan wasu kasashe, da taimakawa rigingimun soji da tayar da rudani a zamantakewar jama’a, kuma ba a iya gano adadi mai yawa na harsasai da suka shiga cikin hannun kungiyoyin ‘yan ta’adda da masu tsattsauran ra’ayi ba, inda suke yin barazana ga zaman lafiya da kwanciyar hankali na kasa da kasa da na shiyya-shiyya. (Mai fassarawa: Ibrahim)