Ministan masana’antu da fasahar sadarwa na kasar Sin Jin Zhuanglong, ya ce Sin za ta gaggauta ci gaba da gina turakun samar da hidimomin yanar gizo masu tsananin tsaro, a bangaren masana’antun fasahohin intanet na 5G, da karfafa hidimomin da fasahohin ke samarwa ga kasar.
Jin Zhuanglong wanda ya bayyana hakan a jiya Lahadi, yayin bude taron baje kolin fasahohin yanar gizo na PT karo na 31, wanda aka kaddamar a birnin Beijing, ya ce Sin za ta kara fadada samar da hidimomin yanar gizo masu inganci, kamar na 5G, da saura fasahohi masu gaggauta samar da hidimar intanet, ta hanyar ci gaba da daga matsayin na’urorin da ake bukata a fannin.
Kazalika za a gina karin rukunonin masana’antun hidimomin yanar gizo na 5G.
Jin ya kara da cewa, kasar Sin na nazari game da sabbin fasahohin intanet na zangon gaba, da sauran fannoni masu nasaba da nasarar hakan, da kuma azamar bincike da samar da ci gaba a daukacin fannonin zango na gaba na fasahohin sadarwa ko 6G a takaice.
Har ila yau, ministan ya ce Sin za ta ingiza samar da sabbin na’urorin yayata bayanai na zamani, da gaggauta cin gajiya daga fasahohin sadarwa, da zurfafa hade sassan manhajojin dake wanzar da gajiyar masana’antun intanet. (Saminu Alhassan)