Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Guo Jiakun, ya ce kasar Amurka ta yi amfani da batun kayayyakin da ake fitarwa zuwa kasashen waje, kamar jerin sunayen kamfanoni, wajen sanyawa sauran sassa takunkumai bisa hujjar “barazana ga tsaron kasa, da kuma keta manufofin diplomassiyar Amurka”, wanda hakan ya zama wani babban mataki na nuna fin karfi.
Guo ya bayyana hakan ne yayin da ya jagoranci taron manema labarai na yau da kullum na yau Laraba, lokacin da yake tsokaci game da matakin Amurka na shigar da kamfanonin Sin fiye da goma, cikin jerin sunayen wadanda ta hana su shigar da hajoji Amurka, bisa jadawalin da ma’aikatar kasuwancin Amurka ta fitar. Game da hakan, Guo ya ce bangaren Sin zai dauki matakai don kiyaye hakki da muradun kamfanonin kasar Sin.
- Kwalara Ta Kashe Mutum 14, Ana Zargin 886 Sun Kamu A Nijeriya – NCDC
- ‘Yan ta’adda Sun Kai Hari Sansanin Sojoji, Sun Kashe Uku A Borno
Dangane da rahoton da Amurka ta fitar game da “ka’idar barazana ta kasar Sin”, Guo Jiakun ya ce, Sin na shawartar Amurka da ta daina kallon dangantakar da ke tsakanin Sin da Amurka da tsohon tunanin yakin cacar baka, ta kuma daina yada kalaman nan na “barazanar kasar Sin”.
Game da tattalin arzikin Asiya kuwa, Guo Jiakun ya ce, kasar Sin za ta sa kaimi ga samun ci gaba mai inganci, da bude kofa ga kasashen waje, da yin hadin gwiwa da sauran kasashen Asiya, wajen ba da sabbin gundumawa, don inganta ci gaban tattalin arzikin duniya. (Safiyah Ma)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp