• English
  • Business News
Wednesday, October 8, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Sin Za Ta Dauki Matakan Da Suka Dace Kan Kamfani Da Wasu Mutanen Amurka Da Suka Shafi Batun Xinjiang

byCGTN Hausa
2 years ago
Sin

LABARAI MASU NASABA

Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata

Wakilin Sin Ya Ba Da Shawarwari Uku Kan Yaki Da Ta’addanci

Dangane da sabon yunkurin da kasar Amurka ke yi na yada labaran karya da suka shafi jihar Xinjiang, mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Mao Ning ta sanar a taron manema labarai da aka saba yi a yau Talata ranar 26 ga wata cewa, kasar Sin za ta dauki matakan da suka dace daidai da doka kan wani kamfanin tattara bayanan sirri da wasu ma’aikata biyu na Amurka, wadanda suka samar da abin da ake kira tushen takunkumin da Amurka ta kakaba wa Xinjiang ba bisa ka’ida ba.

Da take amsa tambayoyin manema labarai, jami’ar ta bayyana cewa, Amurka ta sake kirkiro da yada labaran karya da suka shafi jihar Xinjiang, ta kuma yi amfani da abin da take kira batun kare hakkin bil’adama a jihar Xinjiang a matsayin uzuri na kakaba takunkumi ba bisa ka’ida ba kan jami’ai da kamfanoni na kasar Sin, ta hakan ta tsoma baki a harkokin cikin gidan kasar Sin sosai, da matukar keta dokokin kasa da kasa da ka’idojin da suka shafi huldar kasa da kasa, kana da bata sunan kasar Sin sosai, da lalata hakki da moriyar jami’ai da kamfanonin kasar Sin da abin ya shafa.

  • Sojojin Faransa Sun Kammala Ficewa Daga Nijar Gaba Daya
  • Sin Ta Harba Taurarin Dan Adam 4 Na Binciken Yanayi

An kuma bayar da rahoton cewa, a ranar Jumma’ar da ta gabata bisa agogon wurin, shugaban kasar Amurka Joe Biden, ya rattaba hannu kan “Dokar ba da izini kan tsaron kasa a kasafin kudi ta shekarar 2024”, wadda ta kunshi munanan tanade-tanade da suka shafi kasar Sin. Game da wannan batu, jami’ar ta yi nuni da cewa, kudurin dokar ya yi katsalandan a harkokin cikin gidan kasar Sin, da karfafa goyon bayan Amurka ga Taiwan a fannin aikin soja, wadda ya saba wa manufar kasancewar Sin daya tak a duniya, da kuma sanarwoyin hadin gwiwa guda uku na Sin da Amurka.

Jami’ar ta kara da cewa, kasar Sin ta yi kira ga Amurka da ta cika alkawarin da shugaban kasar ya dauka na cewa ba za ta goyi bayan ‘yancin Taiwan ba, da daina yin amfani da batun Taiwan, tare da daina kawo cikas ga zaman lafiya da kwanciyar hankali a mashigin tekun Taiwan. (Mai fassara: Bilkisu Xin)

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata
Daga Birnin Sin

Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata

October 7, 2025
Wakilin Sin Ya Ba Da Shawarwari Uku Kan Yaki Da Ta’addanci
Daga Birnin Sin

Wakilin Sin Ya Ba Da Shawarwari Uku Kan Yaki Da Ta’addanci

October 7, 2025
Sauyin Yanayi: “Damfara” Ko Gudun Sauke Nauyi?
Daga Birnin Sin

Sauyin Yanayi: “Damfara” Ko Gudun Sauke Nauyi?

October 7, 2025
Next Post
Gwamnati Ta Dakatar Da Daraktocin Hukumar Sufurin Jiragen Sama 5 Sa’o’i Kadan Bayan Sauke Shugabanninsu

Bikin Kirsimeti: Tinubu Ya Yi Allah-wadai Da Hare-haren Filato

LABARAI MASU NASABA

Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata

Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata

October 7, 2025
Wakilin Sin Ya Ba Da Shawarwari Uku Kan Yaki Da Ta’addanci

Wakilin Sin Ya Ba Da Shawarwari Uku Kan Yaki Da Ta’addanci

October 7, 2025
Cika Shekaru 25 Da Kafuwa: ACF Ta Jadadda Kudirinta Na Samun Hadin Kai Da Zaman Lafiya

Cika Shekaru 25 Da Kafuwa: ACF Ta Jadadda Kudirinta Na Samun Hadin Kai Da Zaman Lafiya

October 7, 2025
Sauyin Yanayi: “Damfara” Ko Gudun Sauke Nauyi?

Sauyin Yanayi: “Damfara” Ko Gudun Sauke Nauyi?

October 7, 2025
SSANU, NASU Za Su Gudanar Da Zanga-zanga A Faɗin Nijeriya A Ranar 9 Ga Oktoba

SSANU, NASU Za Su Gudanar Da Zanga-zanga A Faɗin Nijeriya A Ranar 9 Ga Oktoba

October 7, 2025
Daukacin Mambobin Majalisar Kare Hakkokin Dan Adam Ta MDD Sun Amince Da Kudurin Da Kasar Sin Ta Gabatar Kan Kare Hakkokin Tattalin Arziki Da Zamantakewa Da Al’adu

Daukacin Mambobin Majalisar Kare Hakkokin Dan Adam Ta MDD Sun Amince Da Kudurin Da Kasar Sin Ta Gabatar Kan Kare Hakkokin Tattalin Arziki Da Zamantakewa Da Al’adu

October 7, 2025
Ɓatan-dabon Naira Tiriliyan 210: Kamfanin NNPCL Ya Buƙaci A Ƙara Masa Lokaci

Ɓatan-dabon Naira Tiriliyan 210: Kamfanin NNPCL Ya Buƙaci A Ƙara Masa Lokaci

October 7, 2025
Tinubu

Tinubu Ya Nemi Amincewar Majalisa Kan Karɓo Bashin Dala Biliyan $2.347 Da $500m Na Sukuk 

October 7, 2025
Cikar Wa’adin AGOA Ta Nuna Ra’ayin Amurka Kan Afirka

Cikar Wa’adin AGOA Ta Nuna Ra’ayin Amurka Kan Afirka

October 7, 2025
Da Ɗumi-ɗumi: Yakubu Ya Miƙa Ragamar INEC Ga Agbamuche-Mbu A Matsayin Shugabar Riƙo

Da Ɗumi-ɗumi: Yakubu Ya Miƙa Ragamar INEC Ga Agbamuche-Mbu A Matsayin Shugabar Riƙo

October 7, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Go to mobile version