Ma’aikatar sufuri ta kasar Sin ta sanar a yau Jumma’a cewa, kasar za ta fara cajin kudade na musamman na tashar jiragen ruwa a kan jiragen ruwa mallakar kamfanoni da kungiyoyi da kuma daidaikun mutanen Amurka daga ranar 14 ga watan Oktoba.
Sanarwar ta zo ce a matsayin mayar da martani ga matakin da Amurka ta dauka na sanya wa jiragen ruwa na kasar Sin karin kudaden harajin tashar jiragen ruwa bayan wani bincike na sashe na 301, wanda zai fara aiki ranar Talata mai zuwa, kamar yadda ma’aikatar ta bayyana.
Ma’aikatar ta kuma ce, “Wannan mataki ne da ya dace na kiyaye hakkoki da muradun kamfanonin jiragen ruwa na kasar Sin,” inda ta kara da cewa, matakin da Amurka ta dauka ya yi matukar saba wa ka’idojin cinikayyar kasa da kasa da suka dace, da kuma yarjejeniyar sufurin jiragen ruwa ta Sin da Amurka, kana lamarin ya yi mummunan kawo cikas ga harkokin kasuwancin bangaren teku a tsakanin kasashen biyu. (Mai fassara: Abdulrazaq Yahuza Jere)