Ofishin yada labarai na majalisar gudanarwar kasar Sin zai gudanar da taron manema labarai a ranar Alhamis mai zuwa, da misalin karfe 10 na safe domin yin bayani kan shagulgulan al’adu da za a yi na bikin cika shekaru 80 da samun nasarar yakin turjiyar jama’ar kasar Sin kan zaluncin Japanawa da kuma yakin duniya na biyu.
Jami’ai daga ma’aikatar al’adu da yawon bude ido da na hukumar gidan rediyo da talabijin ta kasar, da mataimakin shugaban rukunin gidajen rediyo da talabijin na kasar Sin (CMG), da shugaban gidan adana kayan tarihi na yakin turjiyar jama’ar kasar Sin kan zaluncin Japanawa, za su halarci taron manema labarun.
Za su yi wa manema labarai karin haske kan wani baje koli mai taken tunawa da fitattun ayyukan al’adu da abubuwa masu nasaba da hakan, sannan za su amsa tambayoyi daga manema labarai. (Mai fassara: Abdulrazaq Yahuza Jere)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp