Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin, ya shaidawa manema labarai a yau Alhamsi cewa, Sin za ta gudanar da dandalin koli na hadin kai bisa shawarar “ziri daya da hanya daya” karo na 3, a watan Octoba a birnin Beijing, ba ma kawai domin tunawa da cika shekaru 10 da gabatar da wannan shawara ba, har ma da kasancewar sa wani muhimmin dandali na tattauna hadin kai mai inganci bisa shawarar.
Ban da wannan kuma, game da matakin kayyade samarwa jami’an Sin iznin visa, bisa hujjar yankin Tibet, Wang Wenbin ya ce, ita ma Sin za ta kayyadewa jami’an gwamnatin Amurka, wadanda abin ya shafa iznin visa a matsayin martani.(Amina Xu)