Kasar Sin ta fitar da wasu tsare-tsare domin hanzarta gina wata kasuwar sufuri da za ta kasance mai bude kofa ga ketare, wacce ta hade hanyoyin sufuri da junansu.
Kasar za ta kuma karfafa tare da yi wa jama’a jagoranci don su shiga a dama da su wajen gina layukan dogo, da tafiyar da sufurin jiragen kasa bisa tanade-tanaden dokoki da ka’idoji, kamar yadda wata takarda daga babban ofishin majalisar gudanarwar kasar ta bayyana.
Har ila yau, takardar ta ce za a kara himma wajen bunkasa samar da ci gaba da matsakaiciyar gasa a tsakanin kamfanonin da ke aikin sufurin jiragen kasa, da kuma tallafa wa kwararrun masana’antu don gudanar da sufurin jiragen kasa bisa cin gashin kansu, a tsakanin birane da na cikin biranen har ma da na kewayensu. (Mai fassara: Abdulrazaq Yahuza Jere)