Hukumar kula da zirga zirgar kumbuna masu dauke da ‘yan Sama-Jannati ta kasar Sin, ta ce da karfe 5 da mintuna 17 na yammacin gobe Alhamis, Sin za ta harba kumbon ‘yan Sama-Jannati na Shenzhou-20 daga cibiyar harba kumbuna ta Jiuquan dake arewa maso yammacin kasar Sin.
‘Yan Sama-Jannati Chen Dong, da Chen Zhongrui da Wang Jie ne za su kasance cikin kumbon na Shenzhou-20. Kuma bayan shigar kumbon da’irarsa a tsawon sa’o’i 6 da rabi, zai yi kewaye tare da hadewa da turken waje na tashar binciken samaniya ta Tianhe, ta yadda za a samar da tsarin aikin kumbuna 3, da sassan zaman ‘yan Sama-Jannati 3 a tashar.
A tsawon wa’adin zamansa a da’irarsa, ‘yan Sama-Jannatin Shenzhou-20 za su karbi bakuncin kumbon Tianzhou-9 na dakon kayayyakin aiki, da Shenzhou-21 mai dauke da ‘yan Sama-Jannati. Kazalika, an tsara dawowar ‘yan Sama-Jannatin Shenzhou-20 doron duniya a karshen watan Oktoban shekarar nan. (Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp