Yau Alhamis, kakakin ma’aikatar harkokin wajen Sin Lin Jian, ya gudanar da taron manema labarai na yau da kullum.
Game da tattalin arzikin Sin, Lin Jian ya bayyana cewa, a bara, yawan karuwarsa ya kai daya bisa ukun karuwar na duniya baki daya, bisa saurin karuwar kashi 5.2 cikin dari. A bana kuwa, Sin ta fitar da hasashen samun karuwar tattalin arziki har kashi 5 cikin dari, wanda ya baiwa al’ummar kasa da kasa kwarin gwiwa a karkashin yanayin rashin tabbaci na tattalin arzikin duniya.
- Xi Jinping Ya Nanata Wajibcin Yin Kwaskwarima Da Kirkire-Kirkire Cikin Hakikanin Hali A Lardin Hunan
- An Yi Bikin Mu’Amalar Matasa Da Yaran Sin Da Amurka A Birnin Beijing
Gwamnatin Sin za ta inganta zamanintarwa irin na Sin bisa bunkasuwa mai inganci, da ci gaba da habaka bude kofarta ga kasashen waje, ta yadda za a sanya karin karfi ga ci gaban kasa da kasa, da kuma raba karin damammakin ci gaba tare da kasashen duniya.
Game da bayanin da kwamandan yankin sojan India-Tekun Pasifik na Amurka John Aquilino ya yi don gane da yankin Taiwan, Lin Jian ya bayyana cewa, yankin Taiwan wani bangare ne na kasar Sin, kuma batun yankin Taiwan harkar siyasa ce ta kasar Sin, don haka kasar Sin za ta warware batun yankin Taiwan da kanta, kuma bai dace wasu kasashen waje su tsoma baki a ciki ba.
Don gane da rikicin Falasdinu da Isra’ila, Lin Jian ya ce, bangaren Sin ya nuna adawa, da sukar dukkanin wasu ayyukan cutar da fararen hula, da kuma karya dokokin kasa da kasa. Ya ce ya kamata kasa da kasa su gaggauta yin ayyuka, da daukar matakin tsagaita bude wuta a matsayin abu mafi muhimmanci. Har ila yau, su dauki nasarar samar da agajin jin kai a matsayin nauyi da ya rataya a wuyansu. (Safiyah Ma)