Ma’aikatar kasuwancin kasar Sin ta fitar da sanarwar sauraron ra’ayoyin jama’a a jiya Alhamis, kan takardar sunayen kayayyakin da kasar za ta kayyade fitarwa kasashen waje.
Sanarwar ta ce, ma’aikatar kasuwanci bisa hadin gwiwa da ma’aikatar kimiyya da fasaha da dai sauran hukumomin kasar Sin, sun yi shirin yiwa wannan takardar kwaskwarima bisa dokar cinikin kayayyakin da ake fitarwa ta Sin da ayoyin dokar masu nasaba da shigo da fitar da kayan fasahohi. Gyaran da za a yi a wannan karo zai shigo da sabuwar aya kan fasaha da kuma gyara wata ayar kan fasaha, tare da cire wasu ayoyi 3 a wannan bangare, da zummar samar da sharadi mai yakini ga hadin gwiwar fasaha tsakanin kasa da kasa.
Bisa sanarwar da aka bayar, an ce, za a fara sauraron ra’ayoyin jama’a nan da ran 1 ga watan Fabrairu mai zuwa. (Amina Xu)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp