Gwamnan Jihar Nasarawa, Injiniya Abdullahi Sule, ya rushe Majalisar Zartarwar Jihar tare da sauke Sakataren Gwamnatinsa, Barista Muhammed Ubandoma-Aliyu.
Gwamnan ya sanar da hakan a wani taron gaggawa da aka gudanar a daren Juma’a, bayan tafiyar Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, wanda ya kai ziyara ta kwana ɗaya jihar.
- Sin Za Ta Ji Ra’ayoyin Jama’a Kan Takardar Sunayen Kayayyakin Da Za Ta Kayyade Fitarwa Kasashen Waje
- Tabbas Sin Za Ta Ci Gaba Da Jan Zarenta A 2025
Duk da cewa ba a bayyana dalilin wannan mataki ba, ana ta raɗe-raɗin sake fasalin majalisar saboda zargin rashin ɗa’a daga wasu mambobin majalisar.
Mutane sun kasa kunnuwa domin dalilin da ya sa gwamnan ya ɗauki wannan mataki.