Bisa amincewar majalisar gudanarwar kasar Sin, gwamnatin kasar za ta kafa yankin kare muhallin halittu na Huangyan Dao. Tuni dai aka fitar da sanarwar amincewa da hakan a shafin yanar gizo na gwamnatin tsakiyar kasar Sin, wato www.gov.cn a Larabar nan, bayan da ma’aikatar kare albarkatun kasa ta gabatar da bukatar hakan.
Sanarwar amincewa da wannan bukata, ta ce kafa wannan yanki na Huangyan Dao, muhimmin tabbaci ne ga wanzuwar matakan kare muhallin halittu mabanbanta, bisa daidaito da dorewa. (Mai fassara: Saminu Alhassan)