Mai magana da yawun ma’aikatar cinikayya ta kasar Sin He Yongqian, ta ce kasar za ta aiwatar da matakai na kara daidaita manufar jawo jarin waje a shekarar nan ta 2025, da aiwatar da matakan bude kofa a karin sassa, da kyautata yanayin kasuwanci a fannin.
He Yongqian, wadda ta bayyana hakan yayin wani taron manema labarai da ya gudana a jiya Alhamis, ta ce ya zuwa yanzu kasar Sin ta baiwa wasu kamfanoni masu jarin waje 13 damar shiga hada-hadar inganta hidimomin wayar tarho, yayin da aka kaddamar da ayyuka masu jarin waje sama da 40 a fannin fasahar cin gajiya daga halittu masu rai. An kuma amince da fara aikin cikakkun asibitoci 3 masu jarin waje.
Jami’ar ta kara da cewa a bana Sin za ta fadada sassan bude kofa a fannin ayyukan gwaji, wanda hakan zai mayar da hankali ga sassa kamar na raya ilimi da al’adu. Bugu da kari, a cewar jami’ar, ma’aikatarta ta taimaka wajen warware wasu batutuwa sama da 500, wadanda suka shafi kamfanoni masu jarin waje ta hanyar hawa teburin shawara, tana mai alkawarta aniyar kasar Sin ta ci gaba da aiki tukuru wajen inganta hidimomi, da yanayin gudanar da hada-hadar kasuwanci ga masu zuba jari na ketare. (Saminu Alhassan)