Shugaban hukuma mai lura da hada hadar samar da kudade ta kasar Sin Li Yunze, ya ce kasar za ta kara azamar samar da kudaden gudanar da kamfanoni masu zaman kan su, da kanana da mafiya kankantar sana’o’i.
Li, wanda ya yi tsokacin a Larabar nan, a gefen taron majalisar wakilan jama’ar kasar Sin dake gudana yanzu haka, ya ce Sin za ta kara yawan lamuni da ake baiwa sassa masu zaman kan su, da rage tsadar samar da kudaden sana’o’i, ta yadda hakan zai haifar da karin alfanu ga kamfanoni.
Jami’in ya kara da cewa, kamfanoni masu zaman kan su ne ke da kaso 92 bisa dari na jimillar kamfanonin dake kasar Sin, kuma akwai tarin hanayen jari a mafiya kankantar sana’o’i, da kananan kamfanonin dake kasar. (Mai fassara: Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp