Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Lin Jian ya bayyana a yau cewa, bana shekara ce ta cika shekaru 30 da gudanar da taron harkokin mata na duniya na Beijing. Kuma kasar Sin za ta ci gaba da amfani da damar da aka samu ta cika shekaru 30 da zartas da sanarwar Beijing da shirin ayyuka, da yin kokari tare da kasahen duniya wajen sa kaimi ga raya sha’anin mata na duniya.
Lin Jian ya bayyana cewa, a ranar 24 ga watan Fabrairu, an gudanar da taron tattaunawa kan murnar cika shekaru 30 da zartas da sanarwar Beijing da shirin ayyuka bisa bukatun Sin da wasu kasashen da abin ya shafa, a yayin da majalisar kare hakkin dan Adam ta MDD ta gudanar da taronta karo na 58, inda shugabannin hukumomin MDD mata suka halarci taron tare da gabatar da jawabi.
Lin Jian ya ce, a matsayin ‘yar sama jannati ta farko ta kasar Sin wadda ta shiga sararin samaniya, Liu Yang ta yi jawabi ta kafar bidiyo cewa, tunanin zaman daidaito na sha’anin binciken sararin samaniya na kasar Sin ya nuna cewa, kasar Sin tana kokarin raya sha’anin mata, wato tabbatar da yanayin yin takara cikin adalci ta bisa kyakkyawan tsari, kuma wannan ne aikin da aka gudanar bisa tunanin sanarwar Beijing. (Zainab Zhang)