Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Mao Ning ta bayyana a gun taron manema labaru na yau Litinin cewa, kasar Sin za ta yi amfani da bunkasuwarta wajen ci gaba da samar da dama ga duniya a fannonin kasuwanci, da zuba jari, da kuma samun bunkasuwa.
Bisa rahoton zuba jari na duniya na shekarar 2023 da taron kula da ciniki da bunkasuwa na MDD ya gabatar a kwanakin baya, jarin waje kai tsaye da kasar Sin ta jawo a shekarar 2022 ya karu da kashi 5 cikin dari, inda yawansu ya kai dalar Amurka biliyan 189.1, adadin da ya kafa tarihi. Mao Ning ta bayyana hakan ne yayin da take amsa tambayoyin da aka yi mata game da wannan batu. (Zainab)