A yau Alhamis kakakin hukumar kasuwanci ta kasar Sin ya bayyana cewa, Sin ta lura da cewa gwamnatin Amurka ta sanar da kakabawa wasu sassa harajin kwastan yi min na yi maka. Ya ce ba shakka Sin na matukar adawa da hakan, za kuma ta dauki matakin mayar da martani don kare moriyarta.
Kakakin ya ce, matakin da Amurka ke dauka ya nuna halayyar yin biris da ci gaban da bangarorin biyu suka samu a shawarwarin cinikin da suka rika gudanarwa cikin shekaru baya-bayan nan, da rufe ido kan moriyar da Amurka ta samu a cinikayyar bangarorin biyu. Kazalika, matakin ya sabawa ka’idar cinikayyar kasa da kasa, ya kuma keta moriyar bangarorin da abin ya shafa, kana ya kasance mataki na cin zarafin saura. Don haka, abokan cinikayyar kasar Amurka da dama ke bayyana matukar rashin jin dadi bisa matakin da kasar ta dauka.
- Ƙoƙarin Tsige Sanata Natasha Ya Gaza Cika Ƙa’idar Doka – INEC
- Alhazan Nijeriya Bana Ba Za A Ba Su Guzuri A Hannu Ba, Sai Dai Su Cira Ta Katin ATM – CBN
Kakakin ya kuma kara da cewa, tarihi ya shaida cewa, kara harajin ba zai magance matsalar da ita kanta Amurka ke fuskanta ba, sai dai ma ya illata moriyarta, da haifar da barazana ga bunkasuwar tattalin arzikin duniya, da tsarin samar da kayayyaki na duniya.
Ya ce ba wanda zai ci gajiya daga mummunar takarar cinikayya, balle manufar ba da kariyar cinikayya. Kuma kasar Sin na kalubalantar Amurka da ta soke matakin karin haraji na kashin kai, ta koma teburin shawarwari da abokan cinikayyarta, don magance bambancin ra’ayi bisa ka’idar adalci da daidaito. (Amina Xu)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp