Ministan kudin kasar Sin Lan Fo’an, ya ce kasar za ta samar da karin matakai daban daban na tallafawa bunkasar tattalin arziki. Ministan ya bayyana hakan ne a Asabar din nan, yayin wani taron manema labarai.
Ya ce matakan da za a aiwatar, sun hada da kara yawan lamuni kan babban mizanin jimillar kudaden mayarwa, don maye gurbin wasu boyayyun basussuka dake wuyan kananan hukumomi, da taimakawa wajen kawar musu da hadurran bashi.
- Nazari Kan Bunkasuwar Sin Bisa Yadda Aka Fitar Da Al’ummar Jino Daga Kangin Talauci
- Shin Dawowar Ahmad Musa Za Ta Taimaka Wa Kano Pillars?
Ministan ya ce akwai dama ta kudade daga gwamnatin tsakiya, ta samar da lamuni, da fadada gibin da ake samu. Kaza lika, a bangaren kasuwar sayar da gidaje, ministan ya ce Sin za ta aiwatar da wasu manufofin kudi, da suka hada da samar da takardun lamuni na musamman ga kananan hukumomi, da kudaden musamman, da manufofin haraji na taimakawa daidaita bangaren.
Har ila yau, Sin za ta fitar da takardun lamuni na musamman daga asusun kasa, don tallafawa manyan bankunan kasuwanci mallakin gwamnati, don su samu damar cike gibin kudaden da ake bukata a matakin koli.
Dukkanin matakan a cewar ministan, na da nufin inganta ikon bankuna na jurewa hadurra, da fadada damar iya samar da lamuni, ta yadda za su iya kyautata ba da hidimar bunkasa tattalin arziki mai nasaba da samar da hajoji da cinikayya. (Saminu Alhassan)