Hukumar kwastam ta kasar Sin, ta ce gwamnatin kasar ta sha alwashin sawwakewa a kalla kasashe masu raunin tattalin arziki 16, dukkanin haraji, kan kaso 98 bisa dari na hajojin su dake shiga kasar.
Wata sanarwa da hukumar ta fitar a Litinin din nan, ta ce tun daga ranar 1 ga watan Satumba mai zuwa, wannan tsari zai fara aiki, inda zai taimakawa irin wadannan kasashe da damar shiga kasuwanni cikin sauki, da ingiza ci gaban bai daya, da yayata manufar nan ta gina al’umma mai makomar bai daya ga daukacin bil adama. (Mai fassarawa: Saminu Alhassan daga CMG Hausa)