Babbar hukumar kwastam ta Sin ta sanar da cewa, domin ci gaba da bunkasa ingantaccen tsarin kasuwanci ta intanet tsakanin kasa da kasa, za ta inganta matakan sa ido kan harkokin kasuwanci ta intanet tsakanin kasa da kasa, a fannin fitar da kayayyaki zuwa kasashen ketare.
Sanarwar da hukumar ta fitar jiya Laraba ta ce, daga ranar 15 ga watan Disamban 2024, za a soke ka’idar yin rijistar hajojin da ake fitarwa zuwa dakunan adana kayayyaki da kamfanoni masu sayar da kaya ta intanet tsakanin kasa da kasa suka kafa a ketare. Amma duk da haka, kamfanoni na bukatar isar da bayanai ta intanet game da hajojin dake akwai da wadanda aka fitar daga siton ga hukumar ta kwastam, kuma su ne ke da alhakin tabbatar da sahihancin bayanan. (Safiyah Ma)