Firaministan kasar Sin Li Qiang, ya fada a yau Talata cewa, kasar Sin a shirye take ta kara bayar da goyon baya da zurfafa hadin gwiwa da MDD, domin neman tabbatar da jagorancin duniya mai cike da adalci da daidaito.
Li ya bayyana hakan ne a yayin ganawarsa da babban sakataren MDD Antonio Guterres, a gefen taron kasashen BRICS karo na 17. Ya kuma yi kira ga MDD da ta taka rawar gani a duniyar da take fama da tashin-tashina, yana mai gargadin cewa, duniya na fuskantar karuwar rashin kwanciyar hankali da rashin tabbas. (Mai fassara: Abdulrazaq Yahuza Jere)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp