A ranar Laraba 2 ga watan nan na Oktoba, Sinawa 146, da iyalai 5 na kasashen waje dake zaune a kasar Lebanon, sun iso birnin Beijing lami lafiya, cikin wani jirgin saman shata na kamfanin AIR CHINA.
A halin da ake ciki yanzu, dukkanin Sinawa dake da niyyar ficewa daga kasar Lebanon sun riga su baro kasar cikin koshin lafiya. Rahotanni sun ce ofishin jakadancin kasar Sin dake Lebanon na ci gaba da gudanar da ayyukan da suka rataya a wuyan sa. (Safiyah Ma)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp