• English
  • Business News
Tuesday, October 28, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Sirrin da ke Tattare da Ganyen Mangwaro Ga Lafiyar Ɗan Adam

by Sani Anwar
7 months ago
Mangwaro

Ganyen mangwaro na da matukar amfani ga lafiyar dan’adam, domin kuwa yana kunshe ne da sinadarin ‘antiodidants’ da kuma wasu muhimman sinadarai da ke taimakawa wajen warkar da cututtuka daban-daban.

Ga wasu daga cikin cututtukan da ganyen mangwaron ke amfani wajen warkarwa:

  • Gwarzon Shugaban Kamfani Mallakar Gwamnati Na 2024: Bamanga Usman Jada
  • Nazari Kan Cututtuka 8 Da Ke Kama Zomo Da Hanyoyin Mangance Su

1-Maganin Ciwon Siga (diabetes):

Ganyen mangwaro na dauke da ‘tannins da anthocyanins’, wanda ke taimakawa wajen rage yawan siga a cikin jini.

don haka, a nan sai a nemi ganyen mangwaron kamar guda hudu zuwa biyar, a tsabtace su sai a tafasa su kimanin kofi guda na ruwa. A bar shi ya huce, sai a tace sannan a sha da safe kafin a karya kumallo.

LABARAI MASU NASABA

Gwarzuwar Ma’aikaciyar Jinya Ta Shekarar 2025: Misis Mabel Ijeoma Duaka

Amfanin Yawan Shan Ruwa Da Kuma Illolin Rashin Yawan Sha

Wannan hanya, na matukar taimakawa sosai wajen sarrafa sinadarin insulin a jikin mutum.

 

2-Maganin Hawan Jini (Hypertension)

Ganyen mangwaro na rage matsin jini, sannan kuma yana karfafa jijiyoyin jini.

Saboda haka, a nan sai a nemi sabbin ganyen mangwaro, a tafasa su sosai a tace, sannan a sha rabin kofi da safe da kuma yamma.

 

3-Maganin Basir Sadidan

Idan ana fama da basir, za a iya amfani da ganyen mangwaro don rage kumburi da ciwo.

Bayan an samu wannan ganye na mangwaro, sai a busar da shi a kuma daka shi har sai ya zama gari. kana sai a dauki cokali daya na garin a hada da rabin kofi na ruwan dumi, sannan a zuba zuma a ciki kadan a sha kullum har sai an samu sauki.

 

4-Maganin Cututtukan da ke Cikin Baki

Idan ana fama da kuraje a baki, zubar jini daga hakora ko kuraje a harshe, ganyen mangoro na da matukar amfani wajen magance su.

A nan, tafasa ganyen za a yi a tace, sannan a yi amfani da ruwan wajen wanke baki sau uku a rana. Idan ana so kuma za a iya kara gishiri dan kadan, don karin karfi.

 

5-Maganin kunar Wuta

Idan aka samu kuna, ganyen mangoro na taimakawa wajen rage radadi da saurin warkewa.

Saboda haka, sai a busar da ganyen, a kone shi har sai ya zama toka. Sai a yi amfani da tokar wajen shafawa a wurin da aka konen.

 

6-Maganin Cututtukan da Suka Shafi Ciki

Ganyen mangwaro na taimakawa wajen magance matsalolin ciki, kamar ciwon ciki da kuma gudawa.

A nan za a tafasa ganyen ne, sannan a rika shan ruwan kullum sannu a hankali.

 

7-Rage Zafin Jiki da Rashin Nutsuwa (Stress & Andiety)

Idan ana fama da zafin jiki ko rashin hutu, ganyen mangwaro na taimakawa kwarai da gaske wajen kawar da su.

Za a tafasa shi, sannan a rika shan ruwan ko kuma a rika yin wanka da shi, domin samun nutsuwa.

8-Maganin Cututtukan Huhu (Tari, Mura da Sanyi)

Ganyen mangwaro na taimakawa wajen maganin tari, mura da kuma sanyi.

Ana tafasa shi a sha ruwan, domin rage tari da samun waraka daga cutar mura da kuma ta sanyi.

 

9-Inganta Lafiyar Mahaifa da Haihuwa

Ganyen mangwaro na da matukar amfani ga mata masu fama da matsalolin mahaifa.

Har ila yau, yana taimakawa wajen tsaftace mahaifa da kuma kara samun damar haihuwa.

don haka, a nan sai a tafasa ganyen a tace shi, sannan a rika shan sa da dumi.

 

10-Maganin Makakin Makogwaro da Ciwon Wuya

Idan ana fama da kuraje a makogwaro ko ciwon wuya ko kuma makaki, ganyen mangwaro na taimakawa kwarai da gaske wajen warkar da su.

Saboda haka, sai a tafasa shi sosai a yi amfani da ruwan ta hanyar kurkurawa da safe da kuma yamma.

 

Bugu da kari, ganyen mangwaro na da matukar amfani ga lafiyar jikin dan’adam. Idan ana son cin gajiyar fa’idarsa yadda ya kamata, yana da kyau a rika amfani da shi akai-akai.

Sannan, duk da haka; yana da matukar kyau a nemi shawarar likita kafin

a fara amfani da kowane irin maganin gargajiya.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Gwarzuwar Ma’aikaciyar Jinya Ta Shekarar 2025: Misis Mabel Ijeoma Duaka
Kiwon Lafiya

Gwarzuwar Ma’aikaciyar Jinya Ta Shekarar 2025: Misis Mabel Ijeoma Duaka

October 25, 2025
Amfanin Yawan Shan Ruwa Da Kuma Illolin Rashin Yawan Sha
Kiwon Lafiya

Amfanin Yawan Shan Ruwa Da Kuma Illolin Rashin Yawan Sha

October 19, 2025
Wasu Daga Cikin Muhimman Alamomin Ciwon Kansa
Kiwon Lafiya

Wasu Daga Cikin Muhimman Alamomin Ciwon Kansa

October 11, 2025
Next Post
Abubuwan da Za ki Runguma domin Burge Mijinki

Abubuwan da Za ki Runguma domin Burge Mijinki

LABARAI MASU NASABA

Mutum 18 Sun Mutu, 40 Sun Jikkata A Hatsarin Mota A Kebbi 

An Kashe Mutum 10 A Harin Ramuwar Gayya A Jihar Kebbi

October 28, 2025
Ganduje Na Kara Shan Matsin Lamba A Kan Ya Sauka

Zargin Almundahana: An Ɗage Shari’ar  Ganduje Da Matarsa Saboda Rashin Miƙa Takardu

October 28, 2025
An Fara Biyan Ma’aikata Sabon Mafi Ƙarancin Albashin N70,000 A Borno

Sojoji Sun Kashe Masu Yi Wa ISWAP 4 Safarar Makamai A Borno

October 28, 2025
Mangwaro

APC Ta Yi Barazanar Dakatar Duk Kwamishinan Da Bai Sanya Irin Hular Tinubu Ba

October 27, 2025
An Yi Taron Tattaunawa Tsakanin Kasa Da Kasa A Amurka

An Yi Taron Tattaunawa Tsakanin Kasa Da Kasa A Amurka

October 27, 2025
Wakilan Sin Da Na Amurka Sun Yi Tattaunawa Mai Ma’ana Da Zurfi Da Kuma Amfani

Wakilan Sin Da Na Amurka Sun Yi Tattaunawa Mai Ma’ana Da Zurfi Da Kuma Amfani

October 27, 2025
Ribar Manyan Masana’antun Kasar Sin Ta Karu Da Kashi 3.2 Cikin Dari A Watanni Tara Na Farkon Bana

Ribar Manyan Masana’antun Kasar Sin Ta Karu Da Kashi 3.2 Cikin Dari A Watanni Tara Na Farkon Bana

October 27, 2025
Gwamnan Bauchi Ya Tabbatar Da Burgediya Janar Yake a Matsayin Sarkin Ƙabilar Sayawa

Gwamnan Bauchi Ya Tabbatar Da Burgediya Janar Yake a Matsayin Sarkin Ƙabilar Sayawa

October 27, 2025
Yawan Jigilar Kayayyakin Dake Bukatar Kankara a Kasar Sin Ya Zarce Tan Miliyan 117 a Watannin Yuni Da Yuli Da Agusta

Yawan Jigilar Kayayyakin Dake Bukatar Kankara a Kasar Sin Ya Zarce Tan Miliyan 117 a Watannin Yuni Da Yuli Da Agusta

October 27, 2025
Sin Za Ta Yi Tsayin Daka Wajen Kare Tsarin Cinikayya Tsakanin Mabanbantan Sassa

Sin Za Ta Yi Tsayin Daka Wajen Kare Tsarin Cinikayya Tsakanin Mabanbantan Sassa

October 27, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.