Salamu alaikum masu karatu, barkammu da sake haduwa da ku a wannan makon a cikin shirin na mu mai farin jini da albarka na Ko Kin San.
A yau kuma cikin yardar Allah za mu yi bayani kan sirrin inganta kwanciyar aure. Da farko dai ana so uwargida ki kasance mai yin kitso saboda iska ta rika shiga cikin kanki, kin san kai waje ne da yake rufe ana daure shi, akwai zufa wannan zufar zai iya kawo miki warin kai, amma idan a kitse yake iska za ta rika shiga sannan kuma za ki samu damar gyara shi kafin ki kwanta da maigida, idan kanki a kitse yake ki samu turaren kai wato (hair spray) sai ki rika fesawa a tsaga-tsaga za ki ji yadda kanki zai yi kamshi, idan kuma ba ki da kitso ki san yadda za ki yi kafin ki kwamta da maigida ki taje shi ki dan bubbuda shi sai ki fesa turaren kashin naki ki gyara kai za ki ji yadda ke da kanki gashinki zai baki sha’awa. Kar ki sake ki kwanta da kashinki dukun-dukun duk a murmurde.
Hammata
Sannan idan kin san kina da gashi a hammatarki ki yi kokari kafin ki kwanta ko kin yi wanka ana tsefe shi, sannan kuma ana sa masa mai da yake sa kamshi saboda lungu ne matattara ne na tara zufa saboda ba ko yaushe ake askin ba, misali amma an so a ce kar ki zama kwana 40 baki aske gashin mararki da gashin hammatarki ba, kar ki ga kin yi wanka ki ce ai na yi wanka ba lallai ne sai na sa nasa can ba a’a kafin ki shafe mai ki yi kwalliya waje ne na daukan zufa sai ki ga nan da nan kin yi zufa wannan zufar kuma zai iya ba da wani wari can daban.
Kunne
Sannan sai wuya da bayan kunne wadannan wurare ne ma’abota kai baki guraran, uwargida ki kasance duk inda maigida zai iya kai baki wajen to ya kamata mu tsafta ce shi kar ya yi wari, kar ya ji wari, kar ya ji hamami, wuya yana daya daga cikin inda uwargida za ki gyara, kunne shima haka za ki samu audiga ki gyara cikin kunnanki saboda akwai dattin da baya fita a wanka.
Sannan sai abin da ya shafi gabanki dole ne ya zama wajibi ki gyara nononki fiye da ko kina a jikinki wuri ne mai matukar mahimmanci wanda ko wanne dan’Adam da yadda yake zuwa wa wajan.
Mamanki ko Hantsa
Ta yaya za ki gyara akwai abubuwan da ake saidawa da gogewa ke ko ke da kanki za ki iya gyara nonon ki, za ki samu audiga bayan kin fito daga wanka kisa tawul ki goge ruwan wanka ki dan kunna fanka jikinki ya bushe saboda rashin busar da jiki ya kan kawo wari, amma idan jikinki ya bushe ki ka shafa mai sai ki daga nononki ki samu turarenki oil mai kamshi ki dan goggoga sannan ki samu turaran jiki wato (body spray) ki faffesa ta kasan nononki in sha Allah kin kori wari. Sannan kuma idan kina da hali akwai abubuwan da ake sayarwa daga kan sabulu zuwa mai wadanda za su sa su su yi laushi, su yi santse su yi kyau, za ki iya neman su don ki gyara, kyansu da laushinsu da santsinsu kadai zai iya biyan bukata.
Cibiya
Sannan sai waje na gaba shi ne cibiyarki yana da matukar mahimmanci uwargida ki gyara dukkannin gabanki tun daga wuyanki har kasa wato maranki saboda waje ne mai saurin tura sako wajen abin da maigida yake da bukata ko kuma yake da sha’awa.
Gaba
Sai gabanki, gaba yana da matukar mahimmanci, uwargida kin san lallai lallai babu yadda za’a yi ba’ ajin kamshi ya tashi a gabanki saboda waje ne wanda yake shi ne mabukata sannan kuma matunkuda, mai fitar abubuwa da dama ya kamata duk macen da take da tsafta za ta iya lura da kula da abin da maigidan ta yake so to kar ta kuskura ta bari maigida ya ji wani abu na bashi ko tsami ko wani makamancin haka a abin da ya shafi gaba.
Yatsun Kafa
Sannan sai yatsunki na kafa saboda suma waje ne da yake tura sako ya kamata ki zama mai gyaran farcanki ki wanke su sannan ki yanke ki kuma kankare su. Ya zamana wajibi mu zauna mu nutsu mu san yadda za mu rika gyara kammu na farko idan muka yi wannan tsafta mu kammu za mu ji dadin kammu, sannan kuma za mu ri ka burge maigida ya daina leke-leke ya daina hange-hange idan kuma ya hango ya yi ne bisa Sunnah ba wai don gazawarki ba, ba wai don ya gaji dake ba, ba wai don wani abu da yake kushewa ko yake ki a jikinki ba ko kuma kin kasa. Allah ya sa mu mallaki mazajanmu suma su mallake mu.