Assalamu alaikum masu karatu, barkanmu da sake haduwa da ku a wannan makon a cikin shirin namu mai farin jini da albarka na Ado Da Kwalliya.
Turaren Almiski turare ne mai dimbin tarihi da asali.Ya kasance turare mafi shahara a duniya da yi wa ya fi dukkanin sauran turaruka fintinkau kama daga fannin kamshi, yin suna, da kuma amfani.
- Tinubu, Shettima Da Gwamnonin Na Ganawar Sirri
- Bude Kofofin Kasar Sin Muhimmin Mataki Ne Na Ingiza Ci Gaba Da Wadatar Duniya
Yana da matukar amfani ga mata domin yana sanya nishadi da annashuwa, haka kuma yana janyo hankalin maigida zuwa ga uwargida,
A kasashen Larabawa amfani da Almiski ya zamo al’ada a gare su domin duk wata matar da za ta yi aure ko wacce ta yi aure za ka tarar tana mai amfani da Almiski (Musk dahara) wannan baya rasa nasaba da sanin muhimmancinsa,
Shi Miski ba tsiro ba ne, ana samar da shi ne daga jikin Barewa, kuma Allah ya fade shi a Alkur‘ani.
Shi dai miski turarene me kamshi, kuma mai sa nishadi da annashuwa.
Yana da kyau kwarai da gaske a ce a matsayinki na mace koda yaushe ya kasance kina da miski a dakinki domin ana so ko yaushe ki rinka amfani da shi.
Mun riga mun sani shi kamshi abu ne da yake kara dankon soyayya kuma yake dawwamar da ita, sannan Miski yana dauke da sinadarai da dama da suke ba wa gaban mace kariya daga cututtuka, saboda haka ana so kullum mace ta rinka amfani da shi.
Fa’idarsa:
Yana kara karfin gaban mace, yana maganin aljanu, yakan ma iya kashe aljani idan ana hada shi da Za‘afaran da man Zaitun, sannan ana shafawa, ana kuma iya zuba shi a garwashi a dinga hayaki.
Yana maganin warin gaba idan ana shafawa. Yana maganin namijin dare. Yana taimakawa masu matsalar haihuwa idan suna matsi da shi bayan gama al’ada. Sannan kuma yana kamsasa mahaifa. Yana tsaftace gaban mace, Yana kara dankon soyayya tsakanin ma’aurata. Yana maganin kaikayin gaba da kashe kwayoyin cututtuka.
Yana da kaloli guda hudu ne:
Shi Turaren Almiski launinsa ya kasu kashi hudu;
Akwai fari mai kamar madara mai kauri (white musk) a turance, ba ya saurin narkewa kuma kuskure ne mace ta sanya shi a gabanta.
Idan ko aka saka shi to ba zai narke ba kuma wasu illolin za su iya faruwa, sai dai a shafa shi, a saman gaba da matse-matsi. Shi wannan ba’a sashi a cikin gaba saboda a daskare yake bai fiya narkewa ba, sai dai a shafa shi daga wajen gaba, ko kasan hammata.