Aƙalla sojoji biyu da wasu da ake zargin ’yan Boko Haram ne sun rasa rayukansu a wani mummunan hari da aka kai sansanin sojoji a ƙauyen Izge da ke Gwoza, a Jihar Borno.
Harin ya auku ne da misalin ƙarfe 1 na daren ranar Lahadi, inda maharan da ke kan babura suka harba makamin roka (RPG) a kan sansanin sojin Nijeriya.
- Kudaden Musanyar Kasashen Waje Da Sin Ta Adana Sun Kai Fiye Da Dala Tiriliyan 3.2 A Watanni 16 A Jere
- Ƴan Bindiga Sun Kashe Mutane 4, Sun Sace 45 A Katsina
Wani soja mai muƙamin Kyaftin da wani Kofur na daga cikin sojojin da suka mutu, yayin da dakarun suka kashe ’yan ta’adda da dama a fafatawar.
Shugaban Ƙaramar Hukumar Gwoza, Hon. Abba Kawu Idrissa Timta, ya tabbatar da faruwar harin, amma ya ce ba a tantance adadin asarar rayuka gaba ɗaya ba.
An bayyana cewa da farko ’yan ta’addan sun fi ƙarfi, amma mafarauta da ’yan banga suka shiga suka ba wa sojoji kariya, har suka fatattaki maharan.
Wasu daga cikin maharan sun tsere zuwa dajin Sambisa, bayan da sojoji, mafarauta da mazauna garin suka yi musu kaca-kaca.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp