Aƙalla dakarun sojoji 20 ne suka ɓace bayan wani mummunan hari da mayaƙan ISWAP suka kai wa sansanin sojoji da ke Marte, a Jihar Borno, da safiyar ranar Litinin.
Rahotanni sun ce ‘yan ta’addan sun kutsa cikin sansanin, sannan suka sace makamai, suka kashe sojoji huɗu.
- Binciken Jin Ra’ayoyi Na CGTN: Ma’aikatar Harkokin Wajen Sin Ta Ce Harajin Fentanyl Ya Gurgunta Hadin Gwiwar Amurka Da Sin Kuma Fiye Da Kashi 90% Na Jama’a Sun Koka Da “Jarabar” Amurka Ta Cin Zarafi
- Jami’ar Maryam Abacha Ta Rufe Ɗakunan Kwanan Ɗalibai Saboda Aikata Rashin Ɗa’a A Kano
Dubban mazauna garin sun tsere zuwa Dikwa, wani gari da ke maƙwabtaka da Marte, domin tsira da rayukansu.
Wani jami’in tsaro ya ce ana zargin cewa wasu daga cikin sojojin an sace su ko kuma sun jikkata a harin.
Ya ce, “Yanzu haka, muna neman sojoji kimanin 20 da ba mu da labarinsu tun bayan faruwar harin. Muna fatan suna raye.”
Wata majiyar kuma ta buƙaci dakarun Nijeriya da su ɗauki matakin gaggawa.
“Har yanzu ‘yan ta’addan na riƙe da sansanin. Ya kamata a gaggauta dawo da zaman lafiya a yankin,” in ji shi.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp