Dakarun Sojin Nijeriya tare da haɗin gwuiwar dakarun haɗaka, da kuma taimakon bayanan leƙen asiri daga hukumar DSS, sun kashe ƴan bindiga 45 da ke addabar ƙauyen Iburu da ke ƙaramar hukumar Shiroro a jihar Neja.
Majiyoyin tsaro sun bayyana cewa DSS ta samu bayanan sirri cewa ƴan ta’addan na tafe ne da babura da dama suna shirin kai hari ga Iburu da wasu makwaftan kauyuka, lamarin da ya sa aka sanar da dakarun da ke cikin shiri.
- Shugaban Hukumar DSS Ya Kaddamar Da Cibiyar Koyar Da Addinin Musulunci A Kaduna
- DSS Da Sojoji Sun Kashe ‘Yan Bindiga 45 A Neja
Bayanai sun nuna cewa artabu mai tsanani ya biyo baya a ranar Juma’a, inda dakarun suka kashe aƙalla ƴan ta’adda 45. Majiyoyin sun ce mazauna ƙauyen sun kirga gawarwakin ƴan bindiga fiye da 40, tare da motoci da dama na su da suka lalace a yayin musayar wuta.
A yayin wannan farmaki, an rasa rayukan mambobi biyu na dakarun haɗaka, yayin da wasu huɗu ke karɓar magani sakamakon harbin bindiga a babban asibitin gwamnatin jihar da ke babban birnin jihar Neja.
A tuna cewa a watan Afrilu, Kwanturola Janar na Hukumar Kwastam, Bashir Adeniyi, ya bayyana damuwa kan ayyukan ƴan ta’adda a yankin Babanna da ke kan iyakar jihar Neja, inda ya ce jami’ansa sun tsallake rijiya da baya bayan wata kwanton ɓauna da ƴan ta’addan suka yi musu saboda kwace jarakunan mai 500 da ake kai musu ta hanyar fasa ƙwauri.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp